Tsugune bata kare ba a Libiya | Labarai | DW | 10.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsugune bata kare ba a Libiya

Masu kaifin kishin addini a kasar Libiya, sun sace Firaministan kasar Ali Zeidan, a wani dakin Otel dake babban birnin kasar Tripoli.

Hukumomi a kasar Libiya sun sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun sace Firaministan kasar Ali Zeidan da sanyin safiyar Alhamis, a wani Otel dake Tripoli babban birnin kasar tare da wasu masu tsaron lafiyarsa biyu.

Wata sanarwa da aka buga a shafin sadarwa na Internet mallakar gwamnatin kasar, ta bayyana cewa 'yan bindigar da aka tabbatar da cewa tsofaffin 'yan tawayen kasar ne, sun sace shi inda suka tafi da shi ba tare da sun bayyana inda suka kai shi ba, sai dai sunce sun sace shi ne a dangane da kame Abu Anas al-Liby da Amirka ta yi.

Sace Firaminista Zeidan dai ya zo ne, a dai dai lokacin da masu kaifin kishin addin na kasar ta Libiya ke ci gaba da nuna bacin ransu dangane da kame Abu Anas al-Liby da dakarun musamman na kasar Amirka su kayi, bisa zarginsa da kasancewa dan kungiyar al-Qa'ida,.

Masu kaifin kishin addinin dai na zargin gwamnatin kasar Libiyan, da hada baki da Amirka ko ta hanyar bada damar zuwa a kama shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu