Tsugune ba ta kare ba a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 12.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsugune ba ta kare ba a Cote d'Ivoire

Barazanar boren soji na ci gaba da tada hankali a kasar Cote d'Ivoire a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin duba bukatun sojojin.

Rahotanni daga kasar Cote d'Ivoire na cewa an koma jin karar aman bindigogi a barikin sojan birnin Bouake inda sojoji suka tayar da bore a makon jiya. Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an ci gaba da jin karar bindigogin tun daga daren jiya Laraba har ya zuwa yammacin wannan Alhamis. Wadannan harbe-harbe na wakana ne a daidai loakcin da ministan tsaron kasar Alain-Richard Donwahi ke shirin zuwa birnin na Bouake a gobe Juma'a domin gabatar wa da masu boren abubuwan da gwamnatin kasar ta yi musu alkawari da kuma kawo karshen boren. A makon da ya gabata ne dai Sojojin kasar ta Cote d'Ivoire suka tayar da bore a birane daban daban na kasar suna masu neman a biya musu wasu kudeden alawus da karin albashi da gaggauta kara musu girma da kuma samar musu da gidajen zama.