Tsokacin kungiyoyi masu zaman kansu bisa zaben 2015 | Siyasa | DW | 16.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsokacin kungiyoyi masu zaman kansu bisa zaben 2015

A dai-dai lokacin da gangar siyasar Najeriya kan zaben badi ke fara tashi wasu fitattun ‘yan a siyasa kasar sun fara zawarcin kungiyoyi masu zaman kansu

To wannan yunkuri da irinsa ne na farko da wasu fitattun ‘yan siyasa ke hada kai tare da kungiyoyi masu zaman kansu, domin samar da abin da suka kira sahihin zabe na gari ga siyasar Najeriyar, ta hanyar kulla kawance, da zimmar samun goyon bayan a zaben shugaban kasa na 2015. Lamarin ya kasance wata sabuwar kafa da ta kunno kai a dai-dai lokacin da aka kada gogen siyasar kasar da yanzu man'yan jam'iyyun biyu ne suka mamaye ta, watau PDP da ke mulki da kuma APC ta 'yan adawa.

Wannan kawance da ke adawa da manyan jami'yun PDP da APC da suke ganin ba za su samar da zabi ga ‘yan Najeriya ba, da ma kasa shawo kan matsalolin da a ke fuskanta a kasar, to ko ta yaya suke son goyon bayan kowane dan takara ba tare da la'akari da jam'iyyar da ta tsaida shi ba? Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa na daya daga cikin fitattun 'yan siyasar da suka kula wannan kawance.

"Eh to ai akwai lokacin da za ka tinkari jam'iyya, akwai kuma lokaci da za ka tinkari wani, ko da yake muna hamayya da PDP da APC mun kuma gane cewar sun gaza ba za su iya ba. Amma mun san cewa a ko wacce jam'iyya akwai mutane masu kishin kasa wanda za su iya abinda muke son mu yi. Saboda haka mu zamu zabi ‘yan takaranmu a duk inda suka fito in dai ‘yan kishin kasa ne suna da mutunci kuma sun yi an gani''.

To sai dai sanin cewa a lokutan baya, an yi yunkuri makamancin wannan dabarun amma ba su ci nasara ba. Ko me ya dauki hankali wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka shiga wannan tafiya, sanin cewa ba'a sansu da shiga harkar goyon bayan wani dan takara ba? Mr Richard Yakubu Umaru na cikin kungiyoyin da suka kula wannan kawance na a tafi tare.

"Babban matsalar da muka samu a kasar nan shi ne rashin shugabani na kwarai, lalacewar da muka samu daga wannan matsala ce. To mu muna ganin cewa babban hanyar da za'a bi a magance tabarbarewar da aka samu a kasar nan, shine a samu shugabanni na kwarai. Muddin shugaba ne na kwarai, kuma batun wa zamu zabo har yanzu muna nan kan tantancewa".

A lokutan baya dai kananan jam'iyyun siyasa na adawa sun yi aiki a karkashin gamayyar jamiyyun siyasa na CNPP amma ba tare da kula kawance da kungiyoyi masu zaman kansu ba. Ko dai wata dabara ce ta sake bullo da wancan tsarin a taikaice? Har ila yau ga Alhaji Balarabe Musa.

"Wannan runfa ce ta duk jam'iyyu, wannan ta ware jam'iyyu kamar misali ba ruwanmu da PDP ba ruwanmu da APC, amma CNPP ai ta yarda da jam'iyyu. Don haka mu bama son mu ware ko wane dan Najeriya da ko wace kungiyar Najeriya, wanda zai iya taimaka wa a fitar da Najeriya daga cikin hatsarin da take ciki".

A yanzu dai ‘yan siyasa na ci gaba da baza komarsu tare da kula dabarar yadda za su iya kai wa ga madafan iko, a zaben na 2015 a Najeriya, wanda ake ci gaba da shiryawa da fatan shawo kan kalubalen da ake hangen na tattare da shi.

Sauti da bidiyo akan labarin