Tsohuwar Firaministan Birtaniya Margaret Thatcher ta rasu | Labarai | DW | 08.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohuwar Firaministan Birtaniya Margaret Thatcher ta rasu

Margaret Thatcher ita ce ta kasance mace guda tilo wace ta rike muƙamin Firaminista a Birtaniya, kuma a lokacinta ne ƙasar ta sami bunƙasa sosai a fanin tattalin arziƙi.

British Prime Minister Margaret Thatcher (C) leaves 10 Downing Street for the last time as head of the Government on November 27, 1990 as she goes to the House of Commons for question time and to vote in the party leadership election. (Photo credit should read -/AFP/Getty Images)

Margaret Thatcher

Tsohuwar Firaministan Birtaniya Margaret Thatcher ta rasu sakamakon bugun zuciya.

Margaret Thatcher, mai kimanin shekaru 87 da haihuwa ta rasu a safiyar yau, ta taka rawar gani a harkokin siyasar Birtaniya a lokacin da take kan karagar mulki musamman a fannin bunkasa tattalin Arzikin Birtaniya inda ta mayar da hankali kan muhimmancin biyan kudaden haraji. A wani jawabi da ta yi game da batun haraji Thatcher na cewa:

" Dolene ku san nawa ya kamata ku baiwa kasa a matsayin haraji cikin kudadenku na shiga kuma dolene kusan nawa zaku rinka kashewa iyalanku".

Masarautar Ingila ta bayyana cewa Sarauniya Elizabeth ta Biyu ta girgiza matuka da jin mutuwar Thatcher kuma zata tura sakon ta'aziyyarta zuwa ga iyalanta.

Cikin wata sanarwa da 'ya'yan Thatcher Mark da Carol Thatcher suka bayar, sun bayyana cewa Margaret Thatcher ta rasu a safiyar yau.

Thatcher wadda ta kasance shugabar Jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta zamo mace guda da ta taba zama Firaministan Birtaniya da tafi dadewa a karni na 20.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi