1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Tunisiya ya rasu

Binta Aliyu Zurmi
September 19, 2019

Allah ya yi wa Zine El Abidine Ben Ali tsohon shugaban kasar Tunisiya rasuwa a wannan Alhamis a wani asibiti da ke kasar Saudiya, yana da shekaru 83.

https://p.dw.com/p/3PuYO
Tunesien Ex-Präsident Zine El Abidine Ben Ali gestorben
Hoto: picture-alliance/dpa

Marigayi Zine El Abidine Ben Ali, ya jagoranci kasar ta Tunisiya ne a tsakanin shekarar 1987 zuwa 2011, kuma shi ne shugaban kasa na farko da aka hambarar da gwamnatinsa a guguwar juyin juya hali a shekarar 2011.

Bayan nasarar hambarar da gwamnatin nasa, hakan ya yi sanadiyar kawar da wasu shuwagabanni a yankin irin su Hosni Mubarak na Masar da kuma Moamar Gaddafi na Libiya.

A tsakiyar shekarar 2012 ne aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai sakamakon kama shi da laifin kisan masu zanga-zanga wadanda suka yi sanadiyar gwamnatinsa.

A gobe Juma'a ne za a yi jana'izar marigayi Shugaba Zine El Abidine Ben Ali, sai dai wani batu da ke daukar hankali yanzu shi ne wasiyyar da ya bayar na a binne shi a birnin Makka na kasar ta Saudiyya.