1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon Shugaban Mali Ibrahim Keita ya rasu

Abdul-raheem Hassan
January 16, 2022

Allah ya yi wa tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita rasuwa a gidansa a wannan Lahadin yana da shekaru 76 da haihuwa. Tsohon ministan shari'ar kasar da tsohon mashawarcinsa ne suka tabbatar da rasuwar

https://p.dw.com/p/45bNo
Tsohon shugaban kasar Mali marigayi Ibrahim Boubacar Keita
Tsohon shugaban kasar Mali marigayi Ibrahim Boubacar Keita Hoto: Pool/ABACA/empics/picture alliance

Al'ummar kasar Mali na zaman jimamin rasuwar tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita wanda Allah ya yiwa rasuwa. Marigayi Ibrahim Boucar Keita ya yi fatan samun zaman lafiya a kasar da kuma 'yantar da kasar daga halin fargaba na rashin tsaro da kasar ta sami kanta a ciki amma bai sami ikon yin hakan ba. 

An haifi Ibrahim Boubacar Keita a ranar 29 ga watan Janairu 1945, ya yi makarantar Lycee Askia Mohammed a Bamako da kuma Jami'ar Sorbonne a Paris inda ya sami digiri a fannin tarihi da kuma Ilmin siyasar kasa da kasa. Ya yi aiki a cibiyar nazarin binciken kimiyya ta CNRS a Faransa.

A lokacin da yake shekara 41 da haihuwa ya koma Mali inda ya yi aiki a matsayin mai bada shawara ga gidauniyar raya cigaba ta kungiyar tarayyar Turai inda ya kaddamar da shirin raya cigaba na farko na kungiyar tarayyar turai a Mali. A 1990 tare da sauran masu adawa da mulkin Moussa Traore ya samar da kawancen ADEMA ta wanzar da dimukuradiyya a Mali wadda ta zama jam'iyya mafi girma a kasar a tsawon tarihi inda kuma ya zama firaminista. Sakamakon rashin jituwa a Jam'iyyar ta ADEMA Keita ya yi murabus daga mukaminsa na firaminista a shekara ta 2000 ya kafa jam'Iyyar RPM inda ya zo na uku a takarar shugaban kasa a 2002 wanda Ahmadou Tumani Toure ya sami nasara. 

An zabi Keita shugaban kasa a zaben 2013, a lokacin bikin rantsar da shi ya yi alkawarin maido da martabar Mali yadda za ta zama abar misali a fagen dimukuradiyya a yammacin Afirka.

Wasu 'yan kasar Mali yayin zanga zangar goyon bayan juyin mulkin soji
Wasu 'yan kasar Mali yayin zanga zangar goyon bayan juyin mulkin sojiHoto: Adam Diko

"Ina rantsuwar da Allah madaukakin sarki a gaban jama'ar Mali zan kare martabar kasar nan, zan yi aiki tukuru bil hakki da gaskiya domin kare muradun al'umma da kare cigaban dimukuradiyya da tabbatar da hadin kan kasa da yancin cin gashin kai na kasarmu mai albarka."

An nuna masa kauna da karfafa gwiwa an kuma girmama shi sannan an hambarar da shi. Tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita wanda ake yiwa lakabi da IBK ya taba kasancewa fatan kasar Mali na zaman lafiya. Daya daga cikin manyan kalubalen da ya fuskanta a wa'adin mulkinsa na farko shine matsalar tsaro. Sai dai duk da haka an sake zabar sa a wa'adi na biyu a 2018 inda ya kada babban abokin hamaiyarsa tsohon ministan kudi Soumaila Cisse. Ga abin da yake cewa ga jama'a a lokacin yakin neman zabe.

"Ina kira ga dukkan mata na kasar Mali da ku fito kwanku da kwarkwata a ranar 11 ga watan Augusta ku kada kuri'unku. Ina kira da ku bamu cikakken rinjaye, rinjayen da babu tababa a cikinsa."

Bayan kokarinsa na kawo karshen fadan da ake yi a arewacin kasar Mali, Keita ya kuma yi kokarin kare batun kudin bai daya na CFA da aka gada daga iyayen giji na mulkin mallaka.

Jagoran mulkin sojin Mali Assimi Goita
Jagoran mulkin sojin Mali Assimi GoitaHoto: Annie Risemberg/AFP/Getty Images

"Muna nan ECOWAS a wani mataki na waiwaye da kuma musamman aikin da muka dora alhakinsa akan wasu takwarorin mu shugabannin kasashe na yin tunani a game da kudin bai daya. A saboda haka babu wata matsala, ba tare da wata damuwa ko tashin hankali ba, cikin aminci da abokanmu mun sami fahimtar juna da kwanciyar hankali da wasu suke kishin mu. Ina ganin a tsakanin rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya muna bukatar kwanciyar hankali, wannan a baiyane yake."

IBK ya ci burin a nan gaba zai dinke baraka da samar da dawwamammen zaman lafiya a Mali to sai dai a watan Augustan 2020 sojoji suka shirya juyin mulki suka kuma kame shugaban bayan da yan kasa suka yi ta zanga zangar adawa da gwamnatinsa. IBK ya yi jawabi ta akwatunan talabijin ya baiyana murabus daga karagar mulki yana mai cewa idan wasu daga cikin sojojin mu suna gani ta haka za a kawo karshen lamura, to bani da wani zabi na amince saboda bana so a zubar da jini. 

IBK ya rasu a gidansa yana da shekaru 76 a duniya. Ya shugabanci kasar Mali daga watan Satumban 2013 zuwa Agustan shekarar 2020 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnbatinsa sakamakon mumunar zanga-zanga kan rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa.