Tsohon shugaban Côte d'Ivoire ya amince da tsayawa takara
March 11, 2024Gbagbo, wanda ya fuskanci hukunci a kotun hukunta manyan laifuka dake birnin Hague, ya shaki iskar 'yanci daga kotun a shekara ta 2019, duk da cewa kafin wannan hukuncin kotun Côte d'Ivoire ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 sakamakon mallakar wasu bankuna ta hanyar halasta kudin haram.
Karin bayani: Gbagbo zai iya komawa gida - Ouattara
Tsohon shugaban kasar ya gamu da tirjiya bayan ya fadi zaben 2010, ga Allasane Outtara, inda Gbagbon ya ke sauka daga mulkin wanda hakan ya haifar da tashin hankali a fadin kasar.
Karin bayani: Ouattara ya ce ba zai tsaya takara ba
Babbar jam'iyyar adawar kasar ta Democratic Party of Ivory Coast (PDCI), ta nada Tidjane Thiam a matsayin shugaban jam'iyyar a watan Disambar bara, duk da cewa har yanzu babu tabbacin ko Thiam ko kuma Alassane Ouattara za su tsaya takara a babban zaben 2025.