Tsofon shugaban PDP a Najeriya ya gurfana a gaban kuliya | Labarai | DW | 06.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsofon shugaban PDP a Najeriya ya gurfana a gaban kuliya

Kotu a Najeriya ta gurfanar da tsofon shugaban jam'iyyar PDP na kasa Bello Haliru Mohammed tare da dansa bisa zargin karkata akalar wasu kudade na sayan makammai.

Shi dai Bello Haliru Mohammed wanda tsofon ministan tsaro ne na Najeriya, kuma ya jagoranci yakin neman zabe na tsofon shugaban kasar Goodluck Jonathan a shekarar da ta gabata, a cewar hukumar da ke yaki da cin hanci ta kasar ta Najeriya, tare da dansa Bello Abba Mohammed, sun karbi Naira miliyan 300 daga ofishin mai bai wa shugaban kasa na wancan lokaci shawara a fannin tsaro Kanal Sambo Dasuki, wanda shi ma yake fuskantar tuhuma kan batun karkata akalar kudadan sayan makammai ya zuwa yakin neman zabe na Shugaba Jonathan.