1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Shugaban kasa ya tsige shugabar hukumar Zabe

Salissou Boukari
June 29, 2018

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya tsige shugabar hukumar zaben kasar Charlotte Osei, tareda mataimakan ta biyu daga mukamansu biyo bayan kiranyen da aka yi.

https://p.dw.com/p/30Yv1
Afrika Ghana - Nana Akufo-Addo gewinnt Präsidentschaftswahl
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Thompson

Wani kwamiti da aka kafa domin bincika kararrakin da aka lissafa akanta wanda jigo acikinsu sune rashin kwaramci da da'a da kwarewa da ake zarginta, su ne suka kai ga yanke wannan shawarar a ranar Alhamis. Sai dai ko shin menene tasirin wannan watakin ga lamarin siyasa da ma demokaradiyyar kasar ta Ghana a nan gaba? Daraktar cibiyar yin nazarori akan harkokin EU, hakazalika Malami mai koyar da kimiyyar siyasa a jami'ar Ghana Farfesa Ransford Gyampo, yayi bayani inda yake cewa:

"Gaskiya ban ji dadin wannan al'amari ba, ina ma a ce bai faru ba yin la'akari da barazar da wasu jiga-jigan jam'iyyar NPPN, suka yi na cewa za su yi waje da ita idan suka hau mulki har zuwa ga yadda suka rabe da guzumar suka harbi karsana. Wannan mataki da shugaban ya dauka zai iya gurbata ra'ayoyin jama'a haka zalika zai sanya karbar shawarar da watakila aka yi da kyakkyawar manufa tayi wuyar gaske."

Babbar jam'iyyar adawa ta NDC tayi ca da al'amarin kuma ta ce ba za ta nade hannayenta, kuma ta zuba idanu ba ballantana ma a ce ta yi gum da baki akan wannan batu kamar yadda Mohammad Nazir, daya a cikin manyan masu magana da ya'un jam'iyyar haka kuma kakakin tsohon ministar cinikayya da masana'antu yake cewa:

"Ko da yake zanga-zangar da NDCN tace za ta yi a yau bai kasance ba sakamakon mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasar Paa Kwesi Amissah Arthur, a gwamnatin NDC da ta shude, su ma dai jama'ar kasar sun nuna mabambamtan ra'ayoyinsu."

Yanzu abin zaman jira a gani shi ne yadda lamura za su kasance a wannan mulkin da daukacin jama'a ke cewa na da kamanceceniya da mulkin mallaka a maimakon demokaradiyya. Hakazalika zai zamto wani gwajin gaske ga kwatamcin adalci da shugaba Akufo Addo, zai nuna wajen tinkara da kuma magance batutuwan da za su biyo bayan wannan hukunci.