Tshohon shugaban Izraila Perez ya mutu | Labarai | DW | 28.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tshohon shugaban Izraila Perez ya mutu

Shimon Perez ya mutu a shekaru 93, bayan fama da rashin lafiyar mutuwar bangaren jiki na makonni biyu.

 Tun a ranar 13 ga watan Satumba ne dai, Perez ya ke jinya a wani asibiti a kusa da birnin Tel Aviv.

Kafin mutuwarsa dai, Perez ya kasance daya daga cikin jiga jigan kasar ta Izraela da ya rike muhimman mukamai, daga ciki har da mukamin fraimista sau biyu da shugaban kasa, wanda mukami ne na jeka na yi ka, a tsakanin shekara ta 2007-2014.

A shekarata ta 1994 ne ya samu lambar yabo ta Nobel tare da fraiminista Yitzhak Rabin da shugaban Palastinawa Yasser Arafat, dangane da irin rawa da suka taka a kokarin cimma yarjejeniyar Oslo, da ke hankoron bawa Palastinu 'yancin kai.

Yanzu haka dai shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakonninsu na ta'aziyya zuwa ga hukumomin kasar ta Izraila.