Tshisekedi ya yi afuwa ga fursunonin siyasa 700 | Labarai | DW | 14.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tshisekedi ya yi afuwa ga fursunonin siyasa 700

Shugaban Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya yi afuwa ga 'yan kaso na siyasa 700 da ake tsare da su a gidajen kurkuku tun lokacin mulkin Joseph Kabila.

Daga cikin wadanda aka sako har' da wasu fitatun 'yan siyasa wadanda suka yi adawa da tsofuwar gwamnatin Joseph Kabila. Wadanda suka hada da  Franck Diongo, da Diomi Ndongala da kuma Firmin Yangambi. Tun farko kafin zaben da aka yi a kasar a cikin watan Disambar shekara bara Tshisekedi ya sha alwashin cewar zai saki dukkanin fursunonin siyasar idan har shi ya ci zaben.