1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tshisekedi ya neman mafita ga rikicin Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
February 10, 2023

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi yi amfani da ziyarar da ya kai tsibirin Comoros wajen yin Allah wadai da yakin da ya zargi Ruwanda da haddaswa a gabashin kasarsa.

https://p.dw.com/p/4NKVh
Shugaban Kwango Felix TshisekediHoto: Arsene Mpiana/AFP/Getty Images

A yayin tattaunawa da takwaransa na Comoros Azali Assoumani, Shugaba Felix Tshisekedi ya nemi da ya samar da zaman lafiya a Kwango idan ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) daga Senegal a mako mai zuwa. DR Kwango ta zargi makwabciyarta Ruwanda da goyon bayan kungiyar 'yan tawayen M23, ko da shi ke Kigali ta musanta tare da zargi Kinshasa da hada kai da  tsohuwar kungiyar 'yan tawayen Hutu ta FDLR wajen cutar da Ruwanda.

Dama Tshisekedi ya je Angola a farkon wannan makon domin tattaunawa da shugaba Joao Lourenco, wanda shi ne mai shiga tsakani na kungiyar AU tsakanin Kwango da Ruwanda a rikicin da ya barke a gabashin Kwango.