Tsaurara matakan tsaro a Turai da Amirka
February 24, 2015Al-Shabab ta yi gargadin cewar harin da ta kai a shekaru biyu da suka wuce a cibiyar kasuwanci ta Westgate da ke a Somaliya somin tabi ne ga abinda ta ce tana da niyyar fadada hare haren a cikin kasahen yammancin duniya.
Har yanzu dai jama'a na da mummunar tunani a kan harin Westgate na Nairobi, wanda a ciki kusan mutane guda 67 suka rasa rayukansu.
A cikin hoton bidiyon da kungiyar ta fitar ta ce suna da niyyar kai harin na ta'adanci irin na Kenya a cibiyar kasuwanci ta Amirka da Kanada da Oxford Street a London. Ministan tsaron cikin gida na Amirka Jeh Johnson ya yi kira ga jama'a a kasar da su yi hattara duk da ma cewar ana kallon cewar kungiyar ba ta da karfin da take da shi a da.
Hukumomin tsaron Amirka NSC da kuma FBI sun riga sun samu labarin wannan shela ta Al-Shaabab. Ministan tsaron cikin gida na Amirkan Johnson ya ce za su kara tanadar da matakan tsaro domin tinkarar barazanar ta su.