Tsaurara hukunci ga Falatsinawa masu jifa da duwatsu | Labarai | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaurara hukunci ga Falatsinawa masu jifa da duwatsu

Matasa daga bangaren Falatsinawa sun rika amfani da duwatsu wajen jifan 'yan sandan Isra'ila wadanda da yawansu suka shiga harabar masallacin Al-Aqsa na Jerussalam.

A ranar Laraban nan Firayim Minista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya bayyana cewa za a kara tsaurara hukunci ga wadanda ke amfani da duwatsu wajen jifan Yahudawa, wannan na zuwa ne bayan kwanaki uku da aka dauka ana fafata fada a ciki da harabar masallacin Al-Aqsa na Jerussalam.

Matasa daga bangaren Falatsinawa sun rika amfani da duwatsu wajen jifan 'yan sandan Isra'ila wadanda da yawansu suka shiga harabar masallacin, inda suma suka maida martani da harba musu hayaki mai sa hawaye a rikicin da ya kaure a jiya Talata duk kuwa da kiraye-kirayen kasa da kasa na a yayyafa wa zuciya ruwan sanyi.

Bayanan na Firayim Minista Netanyahu na zuwa ne a lokacin da aka fara wani taro da ya yi da ministocinsa da jami'an tsaro bayan da wani direban mota dan Isra'ila ya rasu sakamakon jifa da aka yi masa yana tuki abin da ya sanya motar ta kwace ya yi hadari.