Tsaro ya fara inganta a Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 07.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaro ya fara inganta a Afirka ta Tsakiya

Dakarun kasar Faransa na yin sunturi a kan titunan Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da nufin kare fararen hula daga kashe-kashen ba gaira da dalili.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a kai dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin dubu daya da 200 zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da yaki ya dai-daita. Tuni da kasar Faransa ma ta tura dakarun sojinta kimanin dubu daya zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, domin dawo da zaman lafiya a daya daga cikin kasashen da ta yiwa mulkin mallaka, a dai dai lokacin da dubun dubatar 'yan kasar ke neman mafaka domin kauracewa rikicin addinin da ya kunno kai a kasar.

A kiyasin da kungiyar bada agaji ta Red Cross ta bayar, ya nunar da cewa a kalla mutane 300 ne suka rasa rayukansu, daga ranar Alhamis din da ta gabata kawo yanzu sakamakon rikicin addinin na baya bayannan a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe