Tsarin shari′a a kasashen Musulmi | Labarai | DW | 30.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsarin shari'a a kasashen Musulmi

Bincike ya gano cewar galibin Musulmi a duniya na bukatar yin aiki da tafarkin shari'a a cikin harkokinsu.

Wata cibiyar binciken mai suna Pew Research Center ta gano cewar galibin al'ummar Musulmai a sassa daban daban na duniya na kauunar ganin ana yin aiki da tsarin shari'ar Musulunci a yankunan su, sai dai kawai suna da sabani ne game da hanypyin aiwaatar da tsarin. Sakamakon b inciken da cibiyar ta gudanar, wanda ya shafi zamanktakewar al'umma da kuma sha'anin siyasa daga shekara ta 2008 zuwa 2012, a kimanin kasashen Musulmai 39, ya gano cewar galibinsu na kaunar cimma wannan burin.

Daga cikin yankunan da cibiyar ta yi wannan binciken dai, harda nahiyar Asiya da Afirka da kuma yankin Gabas Ta Tsakiya, inda kuma al'ummomin yankunan suka nunar da cewar sun fi kaunar tsarin shari'ar Musulunci a matsayin tsarin da hukumomi ke yin aiki da su. A kasar Afghanista dai - alal misali, kaso 99 cikin 100 na al'ummar kasar ne suka nuna kaunar aiwatar da tsarin shari'ar Musulunci wajen harkokin rayuwarsu da kuma na addininsu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar