Asusun tattara kudade don kiwon lafiya a Madagaska
March 8, 2019Talla
A kasashe da dama masu tasowa hasalima kasahenmu na Afirka batun kula da kiwon lafiya abu ne mai wuya, saboda galibi babu tsarin inshora na kiwon lafiya domin daukar nauyin marasa lafiya. Kasar Madagaska na daga cikin kasashen da ake fama da irin wannan matsala, amma dai wani shirin da wata cibiyar binciken kiwon lafiya ta Jamus ta bulo da shi na ba da dama ga al'umma na yin 'yar adashe ta wayar hannu suna tattara 'yan kudadensu da zaran wata larurar ta rashin lafiya ta taso to cibiyar ta kiwon lafiya za ta dauki nauyinsu.