Tsarin dimukaradiyya ya fuskanci koma-baya | Labarai | DW | 13.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsarin dimukaradiyya ya fuskanci koma-baya

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta caccaki shugaban Amirka da wasu shugabannin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki kan rashin kare tsarin dimukaradiyya

Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Human Right Watch ta soki Shugaba Joe Biden na Amirka da wasu shugabannin kasashen Yammacin Duniya kan nuna sako-sako wajen kare tsarin dimukaradiyya da tunkarar kalubale na matsalolin annobar cutar Covid-19 da talauci, da rashin daidaito gami da rashin nuna adalci.

Kungiyar ta nuna yadda ake ci gaba da sayar da makamai ga kasashen da suka yi kaurin suna wajen kare hakkin dan Adam.

A wani rahoton kungiyar da aka wallafa a wannan Alhamis mai shafuka fiye da 750 kungiyar ta nuna yadda ake ci gaba da cin zarafin 'yan adawa da masu kajin kare hakkin dan Adam a kasashen China, Rasha, Belarus da Masar. Sannan an samu raunin tsarin dimukaradiyya a kasashen Hungari, Poland, Brazil, Indiya, har ta Amirka zuwa shekarar da ta gabata ta 2021.