1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsare tsohon ministan kudin Mozambik

Suleiman Babayo
January 9, 2019

Wata kotun kasar Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin goyon bayan cafke Manuel Chang tsohon minitsan kudin kasar Mozambik wanda Amirka ta ba da sammaci saboda almundahana da dukiyar kasa.

https://p.dw.com/p/3BGPG
Südafrika Johannesburg | Prozess gegen Manuel Chang, ehemaliger Finanzminister Mosambiks
Hoto: Getty Images/AFP/W. de Wet


Wata kotun kasar Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin goyon bayan cafke tsohon minitsan kudin kasar Mozambik, Manuel Chang, wanda aka tsare a filin jirgin sama a birnin Johannesburg  bisa zargin almundahana kan makuden kudade.

Lauyoyin Manuel Chang sun ce kama shi a Afirka ta Kudu sakamakon bukatar sammaci daga Amirka abin da suka ce ya saba ka'ida. Sai dai kotun ta yi watsi da zance tana cewa sammacin da aka mika na kama Manuel Chang na kan doka.

Shi dai Manuel Chang ya rike mukamun ministan kudin Mozambik daga shekara ta 2005 zuwa 2015 (na tsawon shekaru 10) kuma Amirka tana zargi ya yi amfani da damar wajen halarta kudaden haram. Tun ranar 29 ga watan jiya na Disamba ake tsere da shi a Afirka ta Kudu.