Tsananin sanyi a Rasha da makwabtanta | Zamantakewa | DW | 26.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tsananin sanyi a Rasha da makwabtanta

Mutane 123 suka rigamu gidan gaskiya a Rasha yayin da 83 suka mutu a Ukraine sakamakon tsananin sanyi da aka shafe shekaru 20 ba a ga irinsa ba a kasashen biyu.

Tsananin sanyi da Rasha da kuma makwabtanta suka samu kansu a ciki na ci gaba da salwantar da rayukan mutane da dama duk kuma ma matakan gaggawa da hukumomi ke dauka. Alkaluman sun nunar da cewar tsananin sanyi ya yi awan gaba da rayukan mutane da dama yayin da ya kwantar da daruruwa a asibitocin a Rasha da ukraine. Ko da shi ke dai an fara samun sa'ida a Moscow babban birnin Rasha, amma kuma tsananin sanyin na ci gaba da kassara sauran sassan kasar. Hasali ma dai rabon da a ga sanyi da kuma zubar dusar kankara irin wanda ake fuskanta a yankin Siberia tun shekaru 20 da suka gabata.

Russland Moskau Kreml Winter Eis Schnee Kälte

Tsananin sanyi ya tsayar da komai a Rasha

A halin yanzu dai zirga zirgar motoci ta tsaya cik a Rasha da ma dai Ukraine da ke makwabtaka da ita sakamakon mamaye hanyoyi da dusar kankara ta yi. Hakazalika kankara ta lullube gidajen wasu kauyawa a yankin Siberiya saboda matsalar jigilar gaz da ake amfani da shi wajen dumama daki da ake da ita. Lamarin da ya yi awan gaba da rayukan mutane 123 a Rasha, yayin da 83 kuma suka kwanta dama a Ukraine. Dadin dadawa ma dai,wasu karin 'yan Rasha 833 na kwance a asibiti sakamakon kamuwa da sanyi da suka yi. Lamarin da ya jefa mazauna wuraren da sanyin ya fi tsanani cikin damuwa sakamakon rashin kayan bukatun yau da kullum da kuma na magance sanyi.

"Ba abin da muke da shi a nan baya ga dussar kankara. Daidai da ruwan sha ba mu da shi. Kaduwar sanyi mu ke yi yanzu haka. Sanyi da ake yi a gidajenmu yanzu haka ba kama hannu yaro. kasa da celcius biyu ake yi a falo na yanzu haka."

Sai dai hukumomi sun fara daukan matakan da suka wajaba, inda suka kwashe 'yan Rasha da tsananin sanyin ke neman kassarawa tare da ba su kulawa da ta dace a makarantu da kuma asibitoci da ta tsugunar da su. Baya ga raba musu barguna domin kare kansu daga sanyi, hukumomi na kuma ba su ci da sha musamma ma dai mata masu juna biyu da kuma kananan yara. A wuraren da sanyin ya fi tsanani a Rashan dai hukumomi sun kafa dokar ta baci tun bayan da mutane dubu hudu suka rasa hanyoyin dumama gidajensu sakamakamon lalacewar bututan iskar gaz. Lamari da daya daga cikin matan da suka ci gajiya ta yaba.

Strommast Winter Schnee Eis Kälte Baum Windrad

Tsananin sanyi ya katse wutar lantarki da isakar gaz

"Mun riga mun shafe kwanaki biyu a wannan makarantar. An samar mana da komai da komai. inda aka tsugunar da mu na da dumi, sannan kuma akwai abinci."

A kasar Ukraine da ke makwabtaka da Rasha ma dai dun kanwar ja ce, inda dussar kankara ta fara zuba ba tare da kakkautawa ba. Lamarin da ya kassara harkokin sufuri a biyu daga cikin yankunan kasar. Kwanaki sama da goma kasar ta Rasha da kuma wasu da ke makobtaka da ita suka shafe suna fuskantar tsananin sanyi. Sai dai kuma hasashen yanayi ya nuna cewar al'amura za su fara inganta bayan yayyafi da zai biyo bayan zubar dusar kankara.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi