Tsamin dangantaka a tsakanin Amirka da Rasha
August 8, 2013Fadar Kremlin ta shugaban kasar Rasha, ta bayyana takaicinta dangane da sanarwar da Amirka ta fitar, ta soke wata ganawar da shugabannin kasashen biyui suka shirya yi a watan Satumba, domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafesu, bisa abin da fadar gwamnatin Amirka ta White House ta ce, rashin samun ci gaba ne a kan batun Edward Snowden, tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka da gwamnatin Rasha ta baiwa mafakar siyasa. Mai baiwa shugaban Rasha shawara a kan hakokin da suka shafi kasashen ketare, ya ce wannan matakin, ya nuna cewar, Amirka ba ta kaunar yin mu'amala da Rasha a matsayin wadanda ke da matsayi iri guda. Sai dai a nashi bangare, shugaba Obama ya zargi fadar gwamnatin kasar ta Rasha da komawa ga zamanin yakin cacar-baka. Idan za ku iya tunawa dai, a makon jiya ne Rasha ta baiwa Snowden mafakar siyasa - ta wucin gadi, tare da yin watsi da bukatar Amirka ta neman a mikashi domin ya fuskanci shar'iar cin amanar kasa, bisa bayanan sirrin da ya kwarmata wa duniya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu