Tsaiko na zirga-zirga a Najeriya saboda matsalar man fetur
March 5, 2015Talla
Matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a najeriya ta janyo tsaiko a kan harkoki na zirga zirga a kasar.Misali a Lagas lamarin ya haddasa tafiyar hawaniya ga sha'anin zirga-zirgar kana kuma frashin sufiri ya hau wanda jama' suke ta yin kuka da rashin man.
Matsalar ta haddasa hauhawar frashin sufiri
A koina a kan tittuna a birnin na Lagas jama'a sun ja dogayen layuka a gidajen mai, sannan kuma mutane na zube barjat kan hanya suna jiran motocin haya na shiga. Waɗanda saboda wannan hali da aka samu kai a ciki frashin sufirin za ƙaru.