Tsabtace kasuwanni don dakile yaduwar Cholera a Ghana | Zamantakewa | DW | 03.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tsabtace kasuwanni don dakile yaduwar Cholera a Ghana

Sakamakon yadda cutar Cholera ke kara yaduwa a kasar, hukumar kula da raya birane da yankunan karkara ta gudanar da wani aikin tsabtace manyan kasuwannin kasar.

A kasuwar Makola Mellenium Market da ke a tsakiyar Accra babban birnin kasar Ghana, mata a kasuwar ne suka fito kwansu da kwarkwatansu domin tallafa wa hukumar gudanarwa birnin na Accra wato AMA da kuma kamfanin tsabtace gari na Zoomlion dangane da matakin da hukmar ta dauka na magance matsalar rashin tsabta. Matsalar kuma da ke kara jefa al'ummar kasar Ghana a cikin wani hali na rashin tabbas, domin kuwa cutar Cholera da kasar ke fama da ita yanzu, cuta ce da ake kamuwa da ita sakamakon rashin tsabta. Madam Maberl Adadevor ita ce shugabar mata 'yan kasuwa a Makola cewa ta yi:

"Muna taimaka wa AMA da Zoomlion game da wannan hidima da ta fara, mun san shara da irin kazanta da ke kewaye da mu bai dace ba. Dangane da hakan ne muka kama musu a lokacin da suke ayyukan karfi, mu kuma muna kwasan shara. Da hakan mun tsabtace cikin kasuwanninmu.

Matakin tsabtace kasuwannin ya samu karbuwa

A can kasuwar Agbobloshie ma da ke a birnin na Accra an amsa wannan kira na tsayar da harkar kasuwancin domin tsabtace muhalli. Madam Adjiewaa mai sayar da kayan lambo ne cewa ta yi.

"Ni ma 'yar kasa ce na bar kayayyakin da nake sayarwa, ni ma ina son kasata ta zama tsabtatacciya. Cututtuka da kasa ke fama da su duk na cikin dalilan da ya sa na bar kayan sayarwa na kama wannan aiki."

A kasuwar unguwar Nima inda babbar motar kwasan shara ce ta yi ta kwasan sharan da matan kasuwar ke kwasowa. Sai dai jami'an hukumar AMA da na kamfanin Zoomlion sun ki cewa uffan saboda a cewarsu ba su samu izinin bayyana ra'ayoyinsu daga magabatansu ba.

Ya yanzu mutane kusan fiye da dubu shida suka kamu da cutar Cholera a kasar Ghana a cikin watanni biyu kacal.

Mawallafiya: Mariam Mohammed Sissy
Edita: Mohammad Nasiru Awal