Trump zai gana da Xi Jinping na Chaina
June 20, 2019Talla
Shugabannin za su tattauna batun zargin kamfanin fasahar sadarwa na Huawei da Amirkan ta yi da leken asiri a taron kasashe masu karfin tattalin arziki da zai gudana a mako mai kamawa. Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Firaiministan Kanada Justus Trudeau a wannan Alhamis.