Trump zai dakatar da TikTok a Amirka | Labarai | DW | 01.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump zai dakatar da TikTok a Amirka

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce zai dakatar da amfani da manhajar TikTok da matasa ke amfani da ita wurin yin barkwanci da hira ta bidiyo.

 A cikin karshen makon nan ne dai ake sa ran shugaban zai sanya hannu a kan dokar da ta haramta amfani da TikTok din.

''Muna nazari a kan Tiktok, akwai yiwuwar za mu dode shi, za mu duba yiwuwar amfani da wani abin na daban, domin abubuwa da dama suna gudana, amma dai lallai muna duba abin da za mu iya sauya wa da TikTok.'' inji Donald Trump

Gwamnatin Amirka dai ta ce kwararru sun tabbatar mata cewa kasar China wadda ta sarrafa manhajar TikTok din za ta iya amfani da damar wurin leken asiri ga a Amirka.