Trump ya yi karin kudin fito daga kashi 10% zuwa 15%
February 21, 2026
Shugaban Amurka Donald Trump ya dage kan shiga yakin kasuwanci da kasashen duniya, bayan sanar da sabon mataki a wannan Asabar na yin karin kudin fito daga kashi 10% zuwa kashi 15% wanda zai fara take-yanke.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kotun kolin Amurka ta bayyana manufofin Trump na tattalin arziki a matsayin masu tsauri, tare da yanke hukuncin cewa galibin karin harajin da ya yi ya sabawa doka.
Kotun kolin Amurka ta ce mafi yawan karin harajin Trump ya sabawa doka
Shugaba Trump ya ce ya dauki wannan matakin na yin sabon karin harajin ne bayan nazari mai zurfi kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma'a, sannan kuma yi wa kotun shagube tare da bayyanata a matsayin wadda ba ta kishin Amurka.
Wannan sabon mataki na Donald Trump zai sa murnar kasashe da dama ta koma ciki, bayan sun yi maraba tare da jinjinawa kotun kolin Amurka kan hukuncin da ya yanke wanda ya nuna haramcin karin harajin shugaba Trump wanda ke kokarin shiga yakin kasuwanci da duniya.