Trump ya sallami mai ba shi shawara kan dabarun mulki | Labarai | DW | 18.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya sallami mai ba shi shawara kan dabarun mulki

Shugaba Donald Trump na Amurka a wannan Juma'a ya sanar da sallamar babban mai ba shi shawara a kan dabarun mulki a gwamnatinsa Stephen Bannon.

Shugaba Donald Trump na Amurka a wannan Juma'a ya sanar da sallamar babban mai ba shi shawara a kan dabarun mulki a gwamnatinsa Stephen Bannon. Ana dai ganin korar mista Bannon ba ya rasa nasaba da kalamansa a kan rikici na nuna wariyar launin fata a jahar Virginia.

Sallamar Bannon na zuwa ne yayin da shugaba Trump ke fuskantar kakkausar suka game da kalaman da ya yi da suke tamkar yana goyon bayan turawa farar fata masu akidar wariyar jinsi.