Trump ya sa hannu kan kudirin komawa aiki | Labarai | DW | 23.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya sa hannu kan kudirin komawa aiki

'Yan majalisar dokokin Amirka sun kada kuri'ar bada dama a kashe kudade kan harkokin gudanarwar gwamnati har zuwa ranar takwas ga watan Fabrairu.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya rattaba hannu kan kudirin doka da ya ba da damar sake bude harkokin gwamnati kamar yadda fadar White House ta bayyana a yammacin ranar Litinin, abin da ke zuwa bayan da 'yan jam'iyyar Democrats da Republican suka amince a kawo karshen kwanaki uku na tsayar da wasu harkokin gudanarwar gwamnati.

'Yan majalisar dokokin na Amirka dai sun zabi kudirin da zai bada dama a kashe kudade kan harkokin gudanarwar gwamnati har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu.

Wannan kudiri dai an mika ga shi ga 'yan majalisar wakilai inda suka kada kuri'a a kansa kafin mika shi ga Shugaba Trump ya rattaba masa hannu. Dubban daruruwan ma'aikatan tarayya ne dai ake sa ran za su koma aiki bayan tsaikon da suka fuskanta ba tare da sun je aiki ba.