1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya soki salon kasuwancin Kanada

Zulaiha Abubakar
June 11, 2018

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya sake fitowa fili ya bayyana gazawar kasar Kanada a kan kasuwanci karkashin jagorancin Firaministan kasar Justin Trudeau.

https://p.dw.com/p/2zFqR
Justin Trudeau und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/B.v.Jutrczenka

A safiyar yau Litinin ce Shugaba Trump ya rubuta a shafin sa na twitter cewar asara ta tabbata ga kasuwancin da ba adalci a cikin sa, wannan furuci ya kara tsamin dangantaka a tsakanin kashashen biyu aminan juna a baya. Tun da fari firaministan kasar ta Kanada ya soki sabon shirin da Trump ya yi barazanar fitowa da shi a kan kudaden shigar kasar Amirka.