1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Toshe kafar intanet ya ja suka a Habasha

Abdul-raheem Hassan
June 2, 2017

Kafofin sada zumunta na zamani irin Facebook da Twitter da sauran kafofi dai ba su da tasiri a Habasha ganin yadda gwamnati ke sa takunkumi kan yadda 'yan kasar ke caccakar gwamnati.

https://p.dw.com/p/2e3Gx
Äthiopien Botschaft Programm Girls Can code
Hoto: US Embassy Ethiopia

A Ranar Talata ce dai aka fara ankara da rashin intanet a Habasha, to sai babu tabbacin gwamnati na da hannu a toshe kafofin. Amma a bara gwamnatin kasar ta dau irin wannan mataki da zimmar katse hanzarin dalibai amfani da yanar gizo wajen satar jarrabawa. Mohammed Negash na sashin Amharik na DW, dan Habasha ne da ke bibiyar al'amarin kasar:

"Hukumomin gwamnati ba su dau alhakin toshe yanar gizo saboda jarrabawar kasa da ke tafe ba, to amma kowa na fadin hakane bisa irin matakin da gwamnatin ta dauka a bara a lokacin rubuta jarrabawar karshe bayan da aka wallafa tambayoyin darusa uku kafin jarrabawarsu a shafukan Facebook. Wannan ya sa ake ganin dalilan toshe kafofin baya rasa nasaba da dakile satar jarrabawar."

Äthiopien Botschaft Programm Girls Can code
Hoto: US Embassy Ethiopia

To sai dai matsalar ta katse aiyukan gudanarwa na yau da kullum na wasu cibiyoyin kasa da kasa da ke kasar, ciki har da wasu ofisoshin jakadanci da na Majalisar Dinkin Duniya.

Kafofin sada zumunta na zamanin irin Facebook daTwitter da sauran kafofi dai ba su da tasiri a Habasha ganin yadda gwamnati ke sa takunkumi kan yadda 'yan kasar ke caccakar gwamnati. Danel Birhane, daya daga cikin masu fafutuka a yanar gizo ya kuma bayyana wa DW yadda matsalar toshe kafofin ya ke shafar su:

"Ba kafar intanet ta salula kadai aka toshe ba, har ma da sauran kafofi. A yanzu ba na iya gudanar da aiki a shafukana balle duba sakon e-mail. A gaskiya abin akwai sarkakiya."

Habasha dai na cikin kasashen duniya da ke fama da karanci karfin intanet, amma suna cikin kasashen farko da suka fara sa wa internet takunkumi baya ga toshe wasu kafofin rediyon kasashen ketere  saboda hana tasirin zanga-zanagar siyasa, inda cikin shakaru uku an kashe sama da masu fafutuka 500.