Kwaskware bangaren shari'a a Poland
July 4, 2018Talla
Matakin nata dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da dubban al'ummar kasar ke ci gaba da yin zanga-zangar neman a saki ragama ga bangaren shari'ar kasar, domin gudanar da aikinsa cikin 'yanci. Gersdorf ta nunar da cewa ta je wajen aikinta ne domin kare kundin tsarin mulkin kasar da kuma tabbatar da bin doka yadda ya kamata.
Gersdorf da sauran abokan aikinta sun nuna tirjiya da manufar gwamnatin kasar ta masu ra'ayin mazan jiya, na tilasta wasu alkalai 27 yin murabus ba tare da lokacin ajiye aikinsu ya yi ba, a wani mataki da gwamnatin ta ce na yi wa bangaren shari'ar kasar kwaskwarima ne.