1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tigray: Amincewa da tsagaita wuta

September 12, 2022

Bayan shafe tsawon shekaru biyu ana dauki ba dadi da dakarun Habasha, 'yan tawayen Tigray sun nuna sha'awarsu ga shirin samar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU.

https://p.dw.com/p/4GiHm
Yankin Tigray mai fama da rikici
Hoto: Ben Curtis/AP/dpa/picture alliance

A cikin sanarwar da hukumomin Tigray suka fitar, ta ce a shirye suke su yi biyayya ga matakan dakatar da yaki da aka cimma tsakanin juna. 

Ita ma dai gwamnatin Habasha a baya-bayan nan ta nuna amincewarta ga tattaunawar zaman lafiya da kungiyar AU shirya kuma ta ce zata hau teburin tattaunawar ba tare da wani sharadi ba.

Moussa Faki Mahamat da ke jagorantar kungiyar AU ya ce ya na maraba da samun damar shiga tsakani tare da yin kira ga bangarorin biyu su gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar gudanar da tattaunawa ta kai tsaye. 

Shi ma dai sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ta ce, Majalisar Dinkin Duniya a shirye ta ke ta bada goyon bayanta ga kungiyar AU da ke shiga tsakani. Tun a watan Nuwambar shekarar 2020 ne dai gwamnatin Habasha da kuma 'yan tawayen yankin Tigray na kasar. Rikicin dai ya haifar da rasa rayukan dubban mutane yayin da wasu miliyoyi suka rasa matsugunnansu a kasa ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.