Thailand na fama da hare-haren bama-bamai | Labarai | DW | 12.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Thailand na fama da hare-haren bama-bamai

Akalla mutane hudu sun rasu a kasar Thailand, sakamakon jerin hare-hare da yammacin ranar Alhamis da kuma safiyar wannan Juma'a a birnin Hua Hin.

Babban darektan 'yan sandan birnin na Hua Hin Janar Sithichai Srisopacharoenrath, ya ce bama-bamai biyu an boye su ne cikin wasu shuke-shuke a wani titi mai cinkoson jama'a inda masu yawon buda ido ke halarta, kuma jami'an tsaro da suka danganta lamarin da wani shiri na neman tada zaune tsaye a kasar, sun ce su na kokarin gano wadanda ke da alhakin kai wadan nan hare-hare.

Akalla kuma mutane 21 sun sami raunuka, cikinsu har da baki 'yan yawon bude ido da suka hada da 'yan kasar Netherlands, Italiya da kuma Jamus.