Thailand: Kotun koli ta ce a kama Yingluck | Labarai | DW | 25.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Thailand: Kotun koli ta ce a kama Yingluck

Alkalin kotun kolin Thailand ya bada umarnin kamo tsohuwar Firaminista Yingluck Shinawatra duk inda aka ganta.

Kotun kolin Thailand ta bada sammacin kamo tsohuwar Firaministar kasar Yingluck Shinawatra bayan da ta ki baiyana a kotun wadda za ta yanke hukunci kan tuhumar da ake yiwa tsohuwar Firaministar kan laifin sakaci da ya shafi yadda gwamnatinta ta aiwatar da shirin tallafi kan shinkafa.

Alkalin kotun kolin ya dage yanke hukuncin zuwa ranar 27 ga watan Satumba.

A cewar alkalin tsohuwar Firaministar ta nemi kotun ta jinkirta hukunci ne saboda larurar ciwon kunne da ta ke fama da ita. sai dai alkalin kotun yace ta gaza baiwa kotu takardar shaidar rashin lafiyar. 

A yanzu dai ana neman ta ruwa a jallo kuma tsananta bincike a kan iyakoki.

Idan aka same ta da laifi za ta fuskanci dauri a gidan yari na kusan shekaru goma.