1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Thailand da Kambodiya sun amince su tsagaita wuta nan take

December 27, 2025

Yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ta tanadi janye sojoji daga sansanonin kan iyaka da kuma sakin sojojin Kambodiya da Thailand ta kama.

https://p.dw.com/p/560W8
Iyakar Kambodiya da Thailand
Iyakar Kambodiya da ThailandHoto: Daniel Ceng/Anadolu Agency/IMAGO

Thailand da Kambodiya sun amince a Asabar din nan da tsagaita wuta nan take kan rikicin kan iyaka da suke gwabzawa, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 47 tare da raba wasu kusan miliyan daya da muhallansu a cikin makwanni uku.

Karin bayani: Kambodiya ta zargi Thailand da kai hari a lardin Siem Reap

Kasashen biyu makwabta da ke kudu maso gabashin Asiya sun sanar da hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fidda da safiyar wannan Asabar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya ruwaito.

Sanarwar mai dauke da saka hannun ministocin tsaron Thailand da Kambodiya ta ce tsagaita wutar zai fara aiki take yanke da kimanin karfe 12 na wannan rana ta Asabar 27 da watan Disamba.

Sanarwar ta kuma shata janyewar sojoji da tone nakiyoyin da bangarorin biyu suka dasa a kan iyakokinsu, da aiki tare wajen yakar aikata laifuka ta yanar gizo da kuma sakin sojojin Kambodiya 18 da Thailand ta kama a cikin kwanaki uku da za su biyo bayan fara aiki da wannan yarjejeniya.