1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masana sun nemi a wadata mata da maganin tazarar haihuwa

Ramatu Garba Baba
October 16, 2019

Masana kimiya sun bayar da shawarar a rage farashin kudin maganin yin tazarar haihuwa don ya wadaci mata, ta hakan za a iya shawo kan barazanar da duniya ke fuskanta daga dumamar yanayi inji sanarwar.

https://p.dw.com/p/3RPNa
Niger Verhütung Frauen Schwangerschaft Kinder Geburt
Hoto: Reuters/S. Malo

A  rahoton da wata Mujallar BMJ and Reproductive Health Medical mai kula da kiddigar al'umma ta birnin New York ta fitar, ta ce kashi arba'in da hudu cikin dari na cikin da mata ke dauka a duniya a bisa kuskure ne.

Rahoton ya nunar da yadda bunkasar al'umma, ke kara bukatun abinci da makamashin girki dana ababen hawa, matsalolin da ke kara ta'azzara dumamar yanayin. Hasashe ya nuna cewa nan da shekaru biyu masu zuwa alkaluman al'ummar duniya zai haura zuwa Biliyan goma daga sama da biliyan bakwai da ke rayuwa yanzu, saboda haka tsarin iyali ya kasance sahun gaba a muradun shawo kan matsalar inji rahoton.