1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniya mai dubarun yaki

Sella Oneko ATB/MNA
January 28, 2021

Ana daukar Taytu Betul a matsayin daya daga cikin shahararrun shugabannin Habasha, mata ce ga sarkin sarakuna Menelik II. Ta taka rawa wajen murkushe 'yan mulkin mallaka na Italiya ita ce kuma ta kafa birnin Addis Ababa.

https://p.dw.com/p/3oWe9
African Roots | Taytu Betul

Wace ce Taytu Betul?

Taytu Betul wata mace ce 'yar kasar Habasha mai kima da daraja wadda tare da mijinta sarkin sarakuna Menelik II suka yi mulkin Habasha daga 1889 zuwa 1913. Ana tuna ta saboda jajircewarta da adawa da kuma nasarar da ta samu a kan sojojin Turawan mulkin mallaka na Italiya da kuma karfin ikonta a kotun sarki. Ita ce ta zabi yankin da a yau ya zama babban birnin Habasha ta kuma sanya masa suna Addis Ababa.

Wace ce Taytu Betul kafin ta zama Sarauniyar sarakuna?

An haifi Taytu Betul cikin iyalan sarauta masu karfin tasiri wadanda ke da dangantaka da daular Sulaimaniya wajen shekarar 1840 ko 1851 a cewar wasu majiyoyi a Debre Tabor wanda ba shi da nisa da kogin Tana. An yi mata auren fari tana yarinya 'yar shekaru 10 da haihuwa, wanda ba abin mamaki ba ne ga yarinya 'yar babban gida a wancan zamani. A bayyana cewa ta yi aure-aure wadanda ba ta ji dadin su ba kafin daga karshe ta auri mijinta na biyar Sarkin daular Shewa wanda daga baya ya zama Sarkin sarakuna Menelik II. A lokacin aurensu ta tara dukiya da kadarori masu yawa.

Yaya aka yi Taytu Betul ta zama mai karfin fada a ji?

Auren Taytu Betul da Menelik hadi ne mai karfi kasancewar bangarorin biyu sun kawo hadaka da kawance a arewaci da kudancin Habasha. Yayin da suka zama Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakunam sun kulla kawance da sarakuna da dama na yankin wasu kawancen lumana wasu kuma bayan an gwabza yaki. Sai dai kuma Taytul Betul ta yi kokarin tabbatar da cewa ba wai ta kasance matar sarki ba kawai, amma ta zama cikin masu bada shawara da kuma cikin mayaka. Masana tarihi sun ce ana kallon ta daidai da Menelik kuma a wasu lokutan ta kan zarta da daukar mataki mai tsauri fiye da mijinta.

Da me Taytu Betul ta fi shahara?

Taytu Betul ta yi fice bisa rawar da ta taka na jagorantar yaki a kan Italiya wanda ya haifar da yakin Adwa. An ce Taytu ta jagoranci runduna ta mayaka 5,000 da dawakai 600 wajen fafatawa da Italiyawa wadanda suke kokarin yi wa habasha mulkin mallaka. Taytu ta dage wajen yin adawa da kulla yarjejeniya da Italiya wadda aka yi wa lakabi da yarjejeniyar Wuchale wadda a takarda ta sanya Habasha karkashin ikon Italiyawa. A lokacin da Menelik da Taytu suka afka yaki ga Italiyawa, Taytu ta taka muhimmiyar rawa da kuma jagorantar rundunar ta zuwa fagen daga. Ta sami gagarumar nasara a wani wuri da Italiya ta gina a Mekelle inda ta murkushe italiyan ta hanyar datse musu hanyoyin samun ruwa.

Taytu Betul, matar sarkin sarakuna Menelik II, ta taka rawa wajen murkushe turawan mulkin mallaka na Italiya.

Shin Taytu Betul mace ce da ta fita daban a zamaninta?

Habasha ta yi shugabanni mata masu karfin iko, iyaye mata ko matan masu mulki da kuma mata da dama da suka shiga aikin soji - watakila ba lallai su dauki makamai ba, to amma sun taimaka wa sojoji wajen girki da share-share da kuma karfafa musu gwiwa. Ba kasafai mata suke jagorantar rundunar mayaka ba kamar yadda Taytu ta yi. A wasu bayanai da suka siffanta yakin Adwa, an baiyana ta a matsayin gwarzuwar yaki, sai dai babu wata shaida da ta nuna ta dauki makami da kanta. Ta iya karatu da rubutu wanda hakan ya sa ta zama ta musamman. Taytu na son yin wasan dara da kuma wakoki.

Me ya faru bayan rasuwar Menelik?

A 1909 Sarki Menelik ya sami shanyewar barin jiki. Ta karbi ragamar gudanar da yawancin ayyuka musamman gudanar da sha'anin mulki. Bayan wasu lokuta masu hamayya da ita a cikin iyalan masarauta suka matsa mata lamba ta yi murabus. Wasu masana tarihi sun yi imanin cewa ta zama mai matukar karfin iko wanda ya sa wasu da dama ba sa son ta a kotun sarki. Lokacin da Menelik ya rasu a 1913 aka fitar da Taytu daga fada kuma karfin tasirinta kuma ya shude. Ta rasu a 1917.

Ta yaya muka san abubuwa da yawa game da Taytu Betul?

Mun sami labari game da ita ta hanyar tarihi na baka da kuma tarihi da aka rubuta sannan kuma da bayanai na hotuna. Jama'a a kotun Habasha da jakadun kasashen waje da fursunonin yaki na Italiya da kuma wasiku da Taytu ta rubuta da kanta sun yi cikakken bayani game da ita. Wani injiniya na Switzerland, Alfred Ilg wanda ya yi hulda da Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakuna shi ma ya tara bayanai da hotunan sarakunan wanda ya ba da haske a kan rayuwar fadar.

Shawarwarin kimiyya a kan wannan mukala sun samu ne daga Farfesa Doulaye Konaté, da Dr Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Tushen Afirka na samun tallafi daga gidauniyar Gerda Henkel.