Tawaye na karuwa a uwar jam′iyar PDP | Siyasa | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tawaye na karuwa a uwar jam'iyar PDP

A wani abun dake zaman kara lalacewar al'amuran PDP mai rikici 'ya'yan majalisar wakilan kasar kusan 60 sun bi sahu a kokarin yiwa uwar jamiyyar su ta PDP tawaye.

Cikin kankanen lokaci dai karamar magana ta zama babba, ba kuma tare da bata lokaci ba, dan hakin da ka raina ya kama hanyar tsone ido a cikin jamiyyar PDP mai mulki da ta zauna ta kalli kara rudewar al'amura a cikin ‘ya'yanta. Sama da yan majalisar wakilan kasar 57 ne dai suka bi sahun wasu yan uwansu na dattawan kasar da suka ce zamani ya sauya, kuma suna neman ganin sauyin har cikin jinin jam'iyyar da ta share shekara da shekaru tana fuskantar zargi na kama karya.

Yan majalisar dai kamar ‘yan uwansu na dattawa sun aiko sako ga fadar gwamantin kasar, dama jami'an tsaron dake zaman karnuka na farauta da ko dai subi sahu a kokarin sauyin nasu ko kuma su gani a kasa na bacin ran majalisar da a cewar Hon Yusuf Shitu Galambi dake zaman danta cikin jihar Jigawa ke iya hadawa da taka birki a cikin harkokin kowa a kasar.

Wahlen in Nigeria Präsident Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

To sai dai koma wane irin tasiri ne dai tsundumar majalisar tarrayar kasar cikin rikicin da ake ta'allakawa da gwagwarmayar mulkin kasar na iya kaiwa ga bada sabon sauyin dake iya shafar harkokin mulkin kasar da ta share tsawon shekaru tana bukatar cigaba. Ya zuwa yanzu dai majalisar wakilan kasar ta Najeriya na zaman tushe na adawa a cikin manufofin gwamantin jam'iyyar PDP da ke da kusan kaso 70 cikin darin na daukacin majalisun kasar biyu.

To sai dai kuma hadewar jam'iyyun adawar kasar wuri guda game kuma da wariyar sabuwar PDP ya kama hanyar maida jam'iyyar PDP marainiya cikin harkokin mulkin kasar. Kawancen sabuwar PDP da ‘yan uwansu na APC dai alal misali na nufin karkata kusan ‘yan majalisu 200 cikin 360 dake dokoki ga kasar ta Najeriya a zauren na wakilai. Abun kuma da a cewar Garba Umar Kari dake zaman masanin harkokin siyasar kasar ta Najeriya, ke iya kawo karshen fatan sauyi na cigaba cikin kasar.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf

Hedikwatar uwar jam'iyar PDP

Ana dai cigaba da kai gwauro da mari a tsakanin dattwan PDP da sauran masu fada cikin kasar ta Najeriya da nufin kaucewa fito na fiton da ko bayan PDP ke iya kaiwa ga kafar ungulu ga tsarin demokaradiyyar da ya samu tagomashi na dubban miliyoyi na dalolin mai amma kuma ya kare da mai dasu na baya ga dangi.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin