Tawadros ya zama saban Paparoman ɗarikar Koptik
November 4, 2012Kiristoci mabiya ɗarikar Koptik na ƙasar Masar sun zaɓi saban Paparoma tsakanin 'yan takara uku wanda suka haɗa da Bishop Raphael na birnin Alkahira, da Tawadros da kuma Raphael Afamena. Kamar yadda dokokin zaɓen suka yi tanadi, wani ɗan ƙaramin yaro mai kimanin shekaru takwas, ya tsamo takarda ɗaya, daga cikin 'yan takara uku, ido rufe.
Bishop Tawadros na Baheira a kogin Nilo yayi nasarar zama saban Paparoman.
Tawadros ya gaji Paparoma Schenuda na uku wanda ya rasu a watan Maris na wannan shekara bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Ya jagorancin ɗarikar Koptik tsawan shekaru 40. Saban shugaban ɗarikar Koptik da aka zaɓan zai kama aiki ranar 18 ga watan da mu ke ciki.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal