Tautaunawar sulhu da kungiyar M23 | Siyasa | DW | 09.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tautaunawar sulhu da kungiyar M23

A ci-gaba da neman warware rikicin kasar Kongo, wakilan bangarorin gwamnati da na mayakan kungiyar M23 na ganawa a kasar Uganda.

Wannan dai shi ne karo na biyu ana zaman sulhun tsakanin gwamnatin Kinshasa da mayakan kungiyar M23 a birnin na Kampala da ke kasar Uganda,kasar da ta amunce ta yi shiga tsakani domin warware bakin zaren duk kwa da zargin da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi mata na kasancewar ta kanwa uwar gami a rikicin na makwabciyarta Kongon.

Francois Rucogoza Konflikt im Kongo PK in Kampala

Wakilan gwamnatin Kongo

An dai fara tautaunawar ne tun a makon da ya shude,to saidai har ya zuwa yanzu,wakilan bangarorin guda biyu basu fara masayar shawarwari ba,abun da kuma wasu masharhanta ke ganin fadar Kinshasan ce ke dari-dari da maganar tsaigaita wuta abun da Abbe malo Malo mataimakin jagoran gwamnatin Kongon ya musanta ya na mai cewar :

"Mai shiga tsakani ya shaida muna bai kai ga wannan matsayin ba tukuna, idan har ya aka kai ga batun,a lokacin zamu duba maganar ciki da wajenta,sannan a lokacin ne kowa zan san shin me ake bukata amman ba wai bukatar wani bangare ba,dan haka ba zan magana akan batun da babu shi cikin tsarin ba."

To sai dai a nasu bangaren wakilan kungiyar mayakan na M23,sun ce su kam a masaniyarsu, batun tsagaita wuta shi ne a sahun gaba ga ajandar tautaunawar inji daya daga cikin wakilan kungiyar ta M23, tsohon dan majalisar dokoki na yankin Kivu Roger Lumbala.

"Wani abu mai mahimmanci a nan shi ne kasancewar bangarorin guda ukku kowa a guri guda,wakilan gwamnatin Kinshasa na nan ,wakilan kungiyar ta M23 na nan, sannan kuma da shi mai shiga tsakani shi ma yana nan. Shi ne mahimmancin abun, ta yadda babu bangaren da zai cewa an bayana wani abu ba shi nan. Mun san tun can farko maganar tsagaita wuta ita ce ke kan gaba ga tautaunawar. Shi ya ke mafarin ba za mu yi wani abun da zai sa mu bari ba a zarge mu da yin zagon kasa ga wannan tautaunawar ba,za mu ci gaba da tautaunawa."

Kongo - Rebellenführer Jean-Marie Runiga

Wakilin kungiyar M23

Bayan da dai aka share kwanaki biyar ana tautaunawar,kawo yabnzu dai babu wata mafita da ake ganin bangarorin za su cimawa a nan gaba, musamman ganin yadda gwamnatin na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ta ki tun can farko ta amunce da batun tsagaita wuta bukatar da 'yan tawayen suka gabatar tun a zagyen farko na tautaunawar, yayin da mai shiga tsakanin ministan tsaro na kasar ta Uganda Cris Pasiyanga, ya bukaci da bangarorin su daidaita kanunsu a jerin abun da za a mai da hankali a kai kamun ya tashi ya zuwa birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin