Tattaunawar Mali ta gamu da cikas | Siyasa | DW | 29.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattaunawar Mali ta gamu da cikas

An tsaida tattaunawar da aka fara a Algiers babban birnin Aljeriya tsakanin 'yan tawayen arewacin kasar Mali da gwamanatin kasar saboda shagulgulan Sallar Layya.

Gamayyar kungiyoyin farar hular kasar sun gudanar da wata tafiyar jerin gwano ta lumana a Bamako fadar mulkin kasar Mali, don nuna adawarsu da duk wata magana ta tsarin fedaraliya ko bada kwarya-kwayar 'yancin gashin kai ga wani yanki na kasar yayin tattaunawar.

A yayin wannan tafiyar jerin gwano da ta hada kungiyoyin farar hula sama da arba'in, ana iya karanta allunan da ke dauke da sakonnin nuna adawa da duk wani tsari na fedaraliya ko bada kwarya-kwaryar cin gishin kai ga wani sashe na kasar. Farfesa Mumuni Sumano malamin ilimin shari'a ne a Jami'ar Bamako ya yi karin haske kan manufar wannan zanga- zanga.

Zanga-zangar fararen hula

"Wannan zanga-zanga da kungiyoyin farar hula suka gudanar na nuni da cewa sun damu ainin da rashin ikon gwamnati a arewacin kasar, sannan dole a magance matsalar tsarin hukuma da siyasa na kasar cikin gaggawa, wannan tafiyar jerin gwano tamkar 'yan kasar Mali na hannun ka mai sanda ne ga tawagogin gwamnati da 'yan tawayen arewacin kasar a wurin tattaunawar da cewa kada a kawo wata magana ta zancen raba kasar".

A farkon makon jiya ne kungiyoyin 'yan tawayen arewacin Mali suka aje bukatar cewa muddin ana son mafita ga wannan tattaunawa dole sai an basu kwarya-kwaryar gashin kai ga yankinsu , abin da tawagar gwamnatin Malin ta yi fatali da shi.

Abin da muhawarar ta kunsa

Fatimata Traore na cikin tawagar gwamnatin Malin a gun tattaunawar Algiers, ta kuma yi karin haske kan tattaunawar.

"Tattaunawar ta shafi mahimman batutuwa hudu ne, na farko maganar tsarin ikon gwamnati da siyasa sai maganar cigaban tattalin arziki da al'adu, sai batun tsaro biye da maganar zaman lafiya da yafe wa juna. Dukan batutuwan an samu cigaba banda sashen sake tsarin hukumar kasar, anan akwai sabani mai yawa tsakanin mu bangaren gwamnati da muka ce za a yi tsarin yanke-yanken jihohi mai karfi, su kuma 'yan tawaye sun kafe kai da fata sai dai a basu kwarya-kwaryar 'yancin gashin kai ko fedaralisme tabbas za a samu mafita, amma yadda suke son nan fa kamar kasa biyu ce".

Domin tafiya da ra'ayin gwamnati dama yawancin 'yan kasar ta Mali, a makon jiya ne al'ummomin yankunan Tombuktu da Gawo da ke arewacin kasar suka gudanar da tasu zanga-zanga mai nuni da cewa basu cikin maganar ballewa ko wai samun kwarya-kwaryar 'yancin gashin kai, kamar yadda tawagar 'yan tawayen ta ayyana a tattaunawar da ake a Algiers babban birnin Aljeriya, kuma wannan batu shine babbar matsala ga tattaunawar.

Sauti da bidiyo akan labarin