1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar matasan kabilu kan magance matsalolin Mali

Abdoulaye Mamane Amadou Mahamadou Kane
November 25, 2019

Daruruwan matasa daga kabilun kasar Mali sun halarci birnin Bamako na fadar gwamnatin kasar domin gudanar da wani gagarumin taro da ya shafi tattaunawa a tsakanin kabilun kasar a wani yunkuri na shimfida zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/3Tfja
Mali Bamako 2018 | Symbolbild Armee | 58. Jahrestag Unabhängigkeit
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

 

Taron na daruruwan matasan daga jinsunan kabilu da dama da galibi ba sa ga maciji da juna a Mali na zuwa ne lokacin da rashin jituwa tsakanin kabilu da aiyukan ta'addanci ke ci gaba da samun gindin zama a kasar.

Fiye da fararen hula 900 suka game da ajalinsu bisa rigingimu masu nasaba da kabilanci a baya, kamar yadda hukumar kula da aiyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, OCHA ke cewa a cikin wani rahoton.

Mali Demonstration für Verbesserung der Infratstruktur
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

Elisabeth Arama daya ce daga cikin matasan da ke halartar taron daga yankin Mopti a tsakiyar Malin mai fama da rikici ta bayyana samun ingantaccen yanayi na zaman lafiya tsakanin kabilun kasar tana mai cewa mutane suna cikin fargaba sakamakon hare-haren da aka fuskanta.

Wata matashiyar mai sunan Fatoumata  da ta fito daga kauyen Tenenkou na tsakiyar Mali na mai ganin duk da kasancewar jami'an tsaro a yankin da take bai hana kasancewarsu a cikin yanayi na fargaba ba.

Mali FAMA Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Mariama Guindo Maiga na daya daga cikin wadanda suka tsara taron na wayar da kan matasa, ta bayyana cewa matsalar tsaron da kasar Mali ta ke fama da shi na ci gaba da haddasa rudani da fargaba a tsakanin kabilun kasar, tana mai cewa tsarin fitowa fili a yi munsanyan bayanai tsakanin kabilun na da matukar muhimmanci.

An dai shirya taron ne karkashin jagorancin kungiyoyin farar hula masu zaman kansu da ke kokarin ganin kabilun kasar sun samu natsuwa da kwanciyar hankali a kasar ta Mali da ke fama da matsalolin tsaro barkatai.