Tattaunawa ta zama dole a rikicin Siriya | Labarai | DW | 29.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa ta zama dole a rikicin Siriya

Waɗannan su ne kallamun da wakilin MDD a Siriya Lakhdar Brahimi ya yi a birnin Mosko inda ya gana da Sergei Lavrov

Manzon masammun na Malalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Siriya Lakdar Brahimi da ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergei Lavrov su dukanin su sun yi amanar cewar bin hanyoyin diflomasiya su ka ɗai ne zasu iya kai ga warware rikicin Siriyar.

Da ya ke yi magana a birnin Mosko a ƙarshen wasu taruruka da ya gudanar da babban jami'n diflomasiyar na ƙasar Rasha Lakdar Brahimi ya ce Siriya na shirin fuskantar wani bala'i idan ba a samu sulhu ba a tashin hankali.Ya ce ''ita hanya kai ɗai hanya ko a fuskanci mumunar bala'i ko kuma a bi hanyoyin neman sulhu ya ce abin na da wahala da sarƙaƙiya amma ba mu da zaɓi.Ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergej Lavrov ya ce ba babban kuskure ya ce dole sai shugaba Bashar Assad ya sauka daga mulki maimakon tattaunawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mahamadou Awal Balarabe