Tattaunawa kan Yankin Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 13.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan Yankin Gabas Ta Tsakiya

Sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry, da takwararsa na Turai Catherine Ashton, sun tattauna batutuwan ƙasashen Larabawa don ganin irin matakan ɗauka

Sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry da babbar Kantomar da ke kula da harkokin wajen Turai Catherine Ashton sun gana a wannan lahadin a birnin Landan, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen Iran, Siriya da Masar, da shirin sulhun Yankin Gabas Ta Tsakiya da sauran batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta faɗawa kamfanin dillancin Associated Press cewa tattaunawar tasu ta yi armashi sosai.

Ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi mai da hankali kai, shi ne yarjejeniyar ƙasar Iran da ƙasashe biyar da ke Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus. An shirya ƙaddamar da tattaunawar ne ranakun talata da laraba a Geneva idan Allah ya kai mu.

Kawo yanzu dai takunkumin ƙasa da ƙasa ya takurawa tattalin arziƙin Iran, kuma Iran na ƙoƙarin sauya wannan lamari ta hanyar sassauta wasu shawarwari da ta yanke a baya.

Kerry da Ashton sun kuma tattauna yunƙurin da suke yi na shirya taron ƙoli kan samar da sulhu a Siriya, da kuma cimma matsaya a siyasance, kan makomar ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu