Tattaunawa kan rikicin Hamas da Isra′ila | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan rikicin Hamas da Isra'ila

A yau ne aka shiga rana ta karshe ta tattaunawar da ake a birnin Alkahiran Masar dangane da lalubo hanyoyi na kawo karshen rikicin da Isra'ila da Hamas ke yi a Gaza.

A yau ne aka shiga rana ta karshe ta tattaunawar da ake a birnin Alkahiran Masar dangane da lalubo hanyoyi na kawo karshen rikicin da Isra'ila da Hamas ke yi a Gaza wanda yai sanadiyyar rasuwar sama da mutane dubu guda.

Daya daga cikin masu shiga tsakani a bangaren Falasdinwa da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya zuwa kammala zaman jiya dai ba a kai ga cimma wata matsaya kwakkwara da za ta kai ga sanya hannu kan wata yarjejeniya ba sai dai ya ce suna fatan cimma nasara a zaman na yau.

Shi kuwa wani wakilin Isra'ila da ke halartar zaman wanda ya zabi a sakaya sunansa ya ce da wuya a iya cimma wata matsaya a karshen zaman domin kuwa gibin da ake da shi na da fadin gaske, hasalima ba wani cigaba na azo a gani da aka samu.

Wannan yanayi da ake ciki dai ya sanya fargaba a zukatan mutane ta sake barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu bayan cikar wa'adi na sa'o'i 72 da aka kebe na tsagaita wuta a rikicin wanda zai kare da misalin karfe 9 na dare agogon GMT.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu