Tattaunar samar da zaman lafiya
September 2, 2010Fraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a shirye ƙasarsa ta ke ta yi na'am da shirin zaman lafiyar da za a cimma domin kawo ƙarshen kaka gidan da Ira'ila ke yiwa Palasɗinu.Shugaban Palasɗiniyawan dai Mahamou Abbas ya ce wajibine Isra'ila ta amince da dakatar da gina matsugunan yahudawa kwata kwata.
da ta ke magana ga shugabannin biyu sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta yi gargaɗin cewa taron da ake yi zai iya kawo canji ga makomar al'umomin yankunan biyusanan kuma ta ci-gaba da cewa
Ta c e ina sane da cewar ba ƙaramin aiki ne ba shawara da za a cimma a wannan tebrin shawarwari, to amma ganin yada har ku ka amince a tattauna wannan wani baban ci-gaba da ke ciki da tarihi ga wannan rikici da aka ƙwashe shekaru ana yi kuma ina jinjinamaku akan wannan kokari.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu