Tattalin arziki
Koma baya a tattalin arzikin Afirka ta Kudu
September 4, 2018Talla
Kasar Afirka ta Kudu ta shiga cikin matsalar koma bayan tattalin arziki da kashi 0.7 cikin 100 kamar yadda alkalun da hukumomin suka fitar suka nuna abin da ke zama nakasu ga Shugaba Cyril Ramaphosa wanda ya dauki madafun iko kasar a watan Febrairun da ya gabata.
Wannan shi ne karo na biyu a zubi hudu na shekara da tattalin arzikin kasra ta Afirka ta Kudu ke samun koma-baya, lamarin da yake da danganta da farin da aka samu a Yammacin Cape da kuma ambaliyar ruwa da ta lalata amfanin gona a gundumar Mpumalanga.
A shekara mai zuwa ta 2019 Shugaba Cyril Ramaphosa na kasra ta Afirka ta Kudu zai fuskanci zabe cikin matsalolin neman masu zuba jari da rashin ayyuka da suka yi wa matasan kasar katutu.