1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin yajin aikin ma'akatan mai a Najeriya

July 2, 2013

A wani abin da ke zaman kama hanyar tabbatar da tasirinta cikin harkokin Tarrayar Najeriya kungiyar kananan ma'aikatan man fetur ta gudanar da yajin aiki da ya gurgunta daukacin al'amura a Abuja.

https://p.dw.com/p/190xT
Nigeria Protest gegen BenzinpreiseHoto: dapd

Duk da cewar kungiyar kananan ma'aikatan man fetur NUPENG ta kirashi na gargadi sannan kuma ta kayyade masa kwanaki, amma kuma sannu a hankali tasirin yajin aikin da suke yi na neman mamaye harkokin Tarrayar Najeriya, inda ya kama hanyar tsayar da al'amuran kasar. Farashin man da ke zaman ruhin 'yan kasar dai ya nunka da kusan kaso 500 cikin dari. Haka ma gidajen mai sun tsayar da sayar da hajar domin bin umarni, a cikin yajin na kwanaki uku da kuma ke da ruwa da tsaki da yanayin aiki dama albashin kananan ma'aikatan.

Duk da cewar tun a shekara ta 2012 aka kai ga cimma yarjejeniya a tsakanin ma'aikatan na karin albashi da kuma tsaida aiki na wucin gadi a cikin masana'antar man dai, amma gazawar hukumomin kasar na tilasta wa kamfanonin man aiwatar da yarjiniyoyin ne dai ya kai ga fara yajin aikin da ke zaman irin sa na farko cikin kusan shekara guda. Wannan yajin dai ya zama wajibi a gudanar da shi a cewar sakataren kungiyar ta NUPENG na kasa comrade Daiyyabu Garga, wanda ya ce tura ta kai bango an kuma kare hakurinsu

MC Lagos Bezinmangel
A bayan fage ake samun mai a biranen da ake yakin aikiHoto: DW

NNPC ta jibge isasshen mai a rumbunta na ajiya

Kaiwa ga ganin baba ko kuma fuskantar matsalar a cikin sauri a yayin da ma'aikatan man Najeriya ke kiran da sake dai, ga dimbin matasa maras aikin yi yajin na zaman sabuwar dama ta rage karfin radadin fatara da talaucin da ta jefa rayuwarsu cikin lahaula; kamar yadda Jamilu Dahiru da ke zaman wani matashin da ya kammalla karatun NCE amma kuma ya kare ya na sai da man a bakar kasuwa ya shaida wa wakilinmu. Sai dai ga mallam Faruk Aliyu da Wakilinmu Ubale Musa ya iske ya yi gumi ya na zaman jiran tsammanin samun man, wai hawoyin sa biyu na zaman na bakar azaba da wuya.

Nigeria Protest gegen Benzinpreise
'Yan Najeriya sun yi zanga-zanga bayan janye tallafin man feturHoto: dapd

A baya dai kasar ta Najeriya da ke takama da bakar hajjar ta mai ta sha fama da rigingimu irin wannan da kan kare a cikin wahala a bangaren daukacin al'umarta. Sai dai kuma a wannan karo kamfanin man kasar NNPC ya ce 'yan kasar su kwantar da hankulansu cikin batu. Duk da cewa jami'an kamfanin sun ki yarda in Deutsche Welle ta dauki muryarsu, amma kuma wani jawabin matsayin na nuna kasar na da isasshen man da zai dauke ta akalla kwanaki 32 cikin rumbunan ajiyar ta.

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mouhamadou Awal