1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakokin Hausa sun kasu dabam-dabam

Abdullahi Tanko Bala AH
June 30, 2020

Masana adabin Hausa sun bayyana irin tasirin da wakoki Hausa ke da su ga zamantakewa irin ta Malam Bahaushe. Misalin irin wannan waka ita ce wakar da Hamisu Yusuf Sa’id Breaker ya yi mai sunan jarumar mata.

https://p.dw.com/p/3ebBW
Hamisu Yusuf Sa’id  (Breaker) matashi mawaki a Najeriya
Hamisu Yusuf Sa’id Breaker matashin mawaki a NajeriyaHoto: Privat

Wakar jarumar Mata ta yi tashe sosai musamman ma a wajen matasa Hausawa, maza da mata, ma’aurata da marasa aure. Wakar ta shiga zukatan matasa Hausawa ka’in-da-na’in, musamman a lokacin bikin Salla karama ta wannan shekara ta Lahadi 24/5/2020 Miladiyya.

Sharhin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero da ke Kano game da wakar jarumar mata

Matasa sun haddace wakar, dangane da soyayya da kauna da son rai dabam-dabam da suke nunawa. Ina iya tunawa a take ko a nazarin wakar baka akwai abubuwa biyu da za a yi la’akari da su a kowace waka da za a yi nazari kuma a karfafa wa mutane su saurare ta.

Sa’idu Muhammad Gusau - Professor an der Bayero Universität Kano
Farfesa Muhammad Sa’idu Gusau, masanin adabin Hausa a jami'ar Bayero da ke KanoHoto: Privat

Akwai wakar da za a yi wa nazari wadda ta dace da al’adu kyawawa na al’ummar Hausawa kuma ta bi sharuda da dokokin addinin Musulunci da Hausawa suka yi imani da shi kuma suke biya. Sannan akwai waka Ballagaza wato ita ce wadda ta saba wa al’adun al’ummar Hausawa da addininsu.

Su kansu kuma zukatan masu sauraron wakokin baka kashi biyu ne. Akwai zukata masu kyau wadanda suke bin kyawawan dokokin al’adu da ka’idojin addinin al’ummarsu. Akwai kuma wasu zukatan wadanda babu ruwansu da dacewar al’adu. A ma’ana ta lugga an bayyana Kalmar Zuciya da wata curarriyar tsoka da take cikin kirjin mutum ko dabba ko tsuntsu wadda ke aika jini zuwa sauran sassan jiki.

Kadan kenan daga cikin nazarin da masanin adabin wakokin Hausa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusauda da ke Jami’ar Bayero a Kano ya yi wa wakar jarumar mata wadda mawaki Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) ya raira.

Domin samun karin bayyani sai a saurari shirin Amsoshin Takardunku a kasa.