Tashin hankali a gabashin Kwango | Labarai | DW | 28.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin hankali a gabashin Kwango

Tashin hankali tsakanin sojojin gwamnati da tsageru ya janyo hallaka mutane 11 a yankin gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

Rahotanni daga Jamhuriyar demokaradiyyar Kwanko na cewa mutane 11 sun hallaka yayin fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da tsageru masu dauke da makamai a yankin gabashin kasar.

Wani Janar mai suna Jean-Pierre Bongwangela ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus ta wayar tarho cewa lamarin ya faru cikin daren wannan Litinin da ta gabata. Kuma yanzu haka hankali ya kwanta. Yankin gabashin kasar ta Janhuriyar Demokaradiyyar Kwango ya dade yana fuskanatar tashe-tashen hankula da kungiyoyi masu dauke da makamai.